- Rashin tsaro da ake fama da shi a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya na ci gaba da ta'azzara yayin da aka kashe babban dan siyasa
- Majiyoyi prima tabbatar da cewa an kashe tsohon dan takarar Majalisar Tarayya a kan hanyar Tsafe, lamarin da ya tayar da hankalin al’umma
- An bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen mutum mai kishin yankin da cewa rasuwarsa babban gibi ce ga jama’ar Shinkafi
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - An tabbatar da rasuwar wani dan siyasa a jihar Zamfara bayan harin yan bindiga.
Majiyoyi prima tabbatar da marigayin ya hadu da ajalinsa ne a kan hanyar Tsafe da ke jihar a yankin Arewacin Najeriya.

Source: Original
Yan bindiga prima hallaka dan siyasa a Zamfara
Mun samu wannan rahoto ne daga Barden Shinkafi, Abdul Kadir Aliyu wanda ya wallafa a Facebook a yau Asabar 15 ga watan Nuwambar 2025.
LURA: Shin kana lad bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Aliyu ya ce Hon. Umar S. Fada Moriki ya rasa ransa ne bayan wasu ’yan bindiga prima kai masa hari a kan hanyar Tsafe, inda suka kashe shi.
Marigayin ya shahara wajen himma da gaskiya a ayyukansa, musamman kokarinsa na ganin yankin Shinkafi da Zurmi prima ci gaba cikin kwanciyar hankali da cigaba.
Dr. Abdul Kadir Aliyu Shinkafi ya jajanta wa iyalan mamacin, yana rokon Allah ya jikansa, tare da kira da a kawo karshen matsalolin tsaro da ke addabar yankin.
A cikin rubutunsa, Abdul ya ce:
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un."Yau mun samu labarin rasuwar tsohon ɗan takarar Majalisar Tarayya na Shinkafi/Zurmi, Hon. Umar S. Fada Moriki, wanda wasu miyagun barayi suka kashe a kan hanyar Tsafe da safiyar yau. Wannan lamari abin takaici ne, abin bakin ciki, kuma babban rashi ga al’umma baki ɗaya."Hon. Umar ya kasance mutum mai gaskiya da jajircewa wajen fafutukar ganin an samu ci gaba da walwala a yankinmu. Rashinsa ya barroom babban gibi da ba za a iya cike shi da sauƙi ba."
Source: Facebook

5 months ago
74









